Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Wasu Ministoci Kan Badakalar Danyen Mai Ganga 48M

0 162

Kwamitin Majalisar Wakilai da ke bincike kan zargin batar gangar danyen mai miliyan 48 ya gayyaci Ministocin Kudi da na Shari’a da wasu manyan shugabannin hukumomin kasar domin bayar da bahasi game da wannan badakalar.

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ne Majalisar ta yanke shawarar fara bincike kan bantan miliyoyin gangar man, wadanda ake zargin wasu manyan jami’an gwamnatin kasar da karkatarwa zuwa China.   

Da yake magana kan rashin girmama gayyatar da kwamitin ta ya yi wa Ministocin Kudi da na Shari’a da wasu jami’an hukumomin gwamnatin kasar, Shugaban Kwamitin Binciken Hon. Mark Gbillah, ya ce ana zargin Ministar Kudi Zainab Ahmed da karya dokar gwamnati ta tsarin fallasa masu yi wa gwamnati zagon kasa ta hanyar kin biyan masu fallasawar adadin kudin da ya dace a ba su.   

Ya ce a daya bangaren kuma, ana zargin Ministan Shari’a na kasa da karbar kudade daga ketare ba tare da sanyawa cikin asusun gwamnati ba.   

Ya kuma bayyana cewa, kwamitin na da bayanan sirri na wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ba su bin ka’idar amfani da tsarin asusun ajiyar kudi na bai-daya.    Sai dai bai bayyana ranar da jami’an gwamnatin za su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: