Majalisar wakilai ta bukaci NUC ta gaggauta dakatar da karin kudin karatu na jami’o’in kasar nan

0 362

Majalisar wakilai ta kasa ta bukaci hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) da ta gaggauta dakatar da aiwatar da karin kudin karatu na jami’o’in kasar nan.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Aliyu Madaki na jamiyyar NNPP daga jihar Kano ya gabatar a zauren majalisar.

Dan majalisar a kudirin da ya gabatar, ya bayyana cewa jami’o’in gwamnatin tarayya a fadin kasar nan sun kara kudin makaranta zuwa kashi 200 cikin 100, tare da bayyana rashin samun kudaden shiga na manyan makarantu da kuma hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan.

Ya kara da cewa an kuma kara kudin dakunan kwanan dalibai.

Madaki ya ce jami’o’in da suka kara kudaden sun hada da Jami’ar Bayero, Kano (BUK), Jami’ar Najeriya Nsukka; Jami’ar Uyo, Jami’ar Maiduguri, da Jami’ar Aikin Gona ta Michael Okpara, da dai sauransu. Ya bayyana damuwarsa kan yadda karin kudaden da jami’o’I ya zo a lokacin da kasar ke fuskantar matsanancin talauci, hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi da hauhawar farashin man fetur sakamakon cire tallafin man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: