Majalisar koli ta shari’a ta yi kira da a sake bibiyar tsarin kundin mulkin kasar nan domin karawa gwamnonin Jihohi karfi iko domin magance matsalolin tsaro da wasu jihohin ke fuskanta.
Cikin wata sako da majalisar ta fitar jiya, ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki dukkan matakan da suka dace domin magance matsalolin tsaro a kasar nan.
Sakon ya bayyana cewa,ya hanyar tattara bayanan sirri da aiki da jami’an tsaro hakan zai magance matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar nan.