Majalisar Kasa ta kare shirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na karbo bashin kimanin naira Triliyan 2
Majalisar Kasa a jiya ta kare shirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na karbo bashin kimanin naira Triliyan 2.
Shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dattijai, Sanata Ajibola Basiru, wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, ya ce babu wata kasa da ba ta ciwo bashi domin cike gibin kasafin kudi.
Basiru ya fadi haka ne daidai lokacin da Darakta Janar ta Ofishin Kula da Bashi ta kasa, Patience Oniha, yayin da take bayar da bahasi game da basussukan Najeriya a watanni uku na farkon shekarar nan a jiya, tace bashin da ake bin Najeriya ya karu daga naira Tiriliyan 32 da biliyan 110 a watan Maris zuwa naira Tiriliyan 35 da biliyan 470 a ranar 30 ga watan Yuni.
Kakakin majalisar ya yi bayanin cewa sabon bashin da shugaban kasar ya nema ya kasance kari ne ga wanda majalisar tarayya ta amince da shi a baya kuma har yanzu yana cikin tsarin rancen kasashen waje na gwamnati.
Shugaban kasa a ranar Talata ya aika da wasika zuwa ga majalisar kasa yana neman a bashi damar ciyo sabbun basuka daga kasashen waje na kimanin naira tiriliya 2.