Majalisar Kasa Na Shirin Zartar Da Babban Kudiri Don Farfado da Noma A Nijeriya

0 211

Kudirin samar da asusun habbaka aikin gona na kasa ya tsalleke karatu na biyu a gaban majalissar Dattawa ta kasa.

Sanata mai wakiltar Nasarawa ta yamma Sanata Abdullahi Adamu wanda shine ya gabatar da kudirin a gaban majalissar yace samar da wannan asusun zai taimaka wajen samar da damammaki a matakai daba-daban na zuba jari a yankunan kasar nan da dama.

Sanata Abdullahi Adamu 

A nasa bangaren shugaban majalissar dattawa sanata Ahmad Lawan yace zuba jari a fannin harkokin noma zai taimaka wajen tabbatar da kudirin Gwamnatin tarayya na samar da isasshen abinci mai ingaci ga kasa.

Ya zuwa yanzu dai an tura wannan kudirin gaban kwamatin kula da habbaka harkokin noma da karkara domin yin nazari a kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: