Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta nanata kudurinta na tallafawa kokarin Ofishin hukumar kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa shiyar Hadejia.
Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abdulkadir Bala Umar T.O, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Kwamandan Shiyar a Ofishinsa.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar Hadejia Muhammad Garba Talaki, ya rabawa manema labarai ciki harda nan gidan Radiyon Sawaba.
Sanarwar ta ce Shugaban Karamar hukumar ya yi alkawarin yin aiki tare da hukumar domin rage karya dokokin tuki daga masu ababen hawa.
Alhaji Bala Umar T.O ya jawo hankalin sabon Kwamandan bisa yadda ake karya dokokin tuki, musamman masu baburan Achaba, da kuma Babur mai kafa 3 wato Keke Napep.
Shugaban Karamar hukumar ya bukaci Kwamandan ya sake kokari domin ganin cewa ya kare rayuka da dukiyoyin Al’ummar yankin.
Kazalika, ya taya sabon Kwamandan murna bisa turoshi yankin nan, tare da masa fatan gudanar da ayyukansa Lafiya.
Tun farko a jawabinsa, Sabon Kwamandan hukumar Engineer Umar Ali, ya ce ya kawo ziyara ofishin shugaban ne domin ya gabatar masa da kansa, tare da neman goyan bayan sa.
Kazalika, ya bada tabbacin cewa zai yi aiki bisa kwarewa domin ciyar da yankin gaba.