Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta nanata jajircewarta wajen tabbatar da tsaftar jiki da ta muhalli
Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta nanata jajircewarta wajen tabbatar da tsaftar jiki da ta muhalli a fadin karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar, Abdulkadir Bala Umar T.O ya bayyana haka jim kadan bayan ya bayar da umarnin rufe gidan wanka da bahaya na ‘Yan Baga, a wata ziyarar bazata da ya kai Kasuwar Jan Bulo a Hadejia.
Yace an rufe gidan wankan har sai baba ta gani, saboda rashin tsaftar muhalli da gudanar da ayyukan da basu kamata ba a harabar gidan.
Yace majalisar baza ta lamunce irin haka ba daga dukkan wani gidan wanka da bahaya ko wajen taruwar jama’a, domin tabbatar da tsafta.
Ya umarci sashen ruwa da tsafta na karamar hukumar da ya binciki dukkanin gidajen wanka da bahaya.
Kazalika, shugaban karamar hukumar ya kaddamar da aikin kwashe ruwan kududdifin Walawa da na Garko domin magance barazanar ambaliyar ruwa.
Yace an dauki matakin domin rigakafin dakile ambaliyar dake faruwa kowace shekara, wacce ta lalata dukiya kuma take barazana ga rayukan jama’a.