Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta kaddamar da kwamitoci guda biyu domin inganta samar da kudaden shiga

0 171

Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta kaddamar da kwamitoci guda biyu domin inganta samar da kudaden shiga na cikin gida ga majalisar.

A jawabinsa wajen kaddamarwar, Shugaban Majalisar Alhaji Abdulkadir Umar T.O ya ce an kafa kwamitocinne domin tallafawa majalisar a shirye-shiryen ta na samar da cigaba.

Ya ce bisa la’akari da koma bayan tattalin arziki na yanzu, dole majalisar karamar hukumar ta inganta hanyoyin tattara kudaden shiga domin cimma manufofinta.

Ya umarci mambobin kwamitocin da su kasance masu gaskiya da kuma sadaukar da kansu duk da nauyin da aka dora musu.

Bala Umar T.O ya ce ana sa ran mambobin kwamitin za su yi aiki tare da tattara rahoton su cikin kwanaki 10.

Kwamitocin biyu sune na kantunan maganin turawa da na musulunci, wanda Alhaji Adamu A. Yaro yake a matsayin Shugaba da Abba Muhammed, Sakatare, yayin da daya kwamiti shine na Shagunan Kananan Hukumomi tare da Alhaji Zakar Shehu a matsayin Shugaba da Muhammad Baffa, Sakatare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: