Shugaban Majalisar dokokin jihar kano Hamisu Ibrahim Chidari ya amince da kudurin gyaran dokar masarautu ta 2019, inda ta zama doka a zaman majalisar.
Sakataren yada labarai na majalisar Uba Abdullahi wanda ya sanar da haka a wata sanarwa, da ya fitar yace, an amince da kudurin bayan doguwar muhawara a lokuta da dama tsakanin kwamitocin majalisar.
Yace majalisar ta samu takarda daga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayyana nadin Mahmoud Balarabe bayan tantancewa a matsayin shugaban hakumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar.
Abdullahi ya yi bayanin cewa kwamatin lura da yaki da cin hanci da rashawa na majalisar ta himmatu wajen daukar mataki na gaba dangane da takardar. Haka kuma majalisar ya samu wata takarda daga ofishin gwamnatin jihar kan kudurin samar da hanyoyin sufiri a yankunan karkara, wanda yace majalisar na aiki akan ta.