Majalisar dokokin jihar Jigawa ta kafa kwamatin wucin gadi domin nazari kan dokar hukumar zabe

0 315

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta kafa kwamatin wucin gadi domin nazari kan dokar hukumar zabe ta jiha da kuma dokar kananan hukumomi dan samar da mafita dangane dacewa ko rashin dacewar gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar nan.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kananan hukumomi na majalisar dangane da bukatar da majalisar bada shawarwari ga jam’iyun siyasa reshen jihar Jigawa ta gabatarwa majalisa kan bukatar dage zaben kananan hukumomi a halin yanzu.

Da ya ke gabatar da rahon, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana bukatar nuna goyon baya ga bukatar da majalisar bada shawarwari ga jam’iyun siyasa ta kasa reshen jihar Jigawa ta mikawa majalisar.

Bisa la’akari da babutuwan da suka shafi siyasa da tattalin arziki a matsayin abubuwan da za su kawo cikas wajen gudanar da zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: