Majalisar dinkin duniya tayi Allah wadai da hukuncin Taliban na hana wata aiki a kungiyar.
Sakataran Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres yayi Allah wadai da gwamnatin kasar Taliban din bisa daukar wannan mataki, yana mai cewa hakan take yancin dan adam na kasa da kasa ne.
Yace mata suna yiwa majalisar dinkin duniya amfani sosai a kasar.
Taliban ta hana mata yanci tun bayan da ta kwace mulkin kasar a shekarar 2021.
Majalisar dinkin duniya tana bada agaji ga mutane Milyan 23 a kasar Afganistan,wanda ke bukatar agajin gaggawa.
Matan da suke yiwa majalisar dinkin duniya aiki na taka muhimmaniyar rawa musamman wajen tsakulo matan dake bukatar agaji.
Tun bayan da Taliban ta karbe ikon kasar ta hana mata zuwa makarantu, kwalejoji da jami’o’i.
- Comments
- Facebook Comments