Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kame wasu lauyoyi da aka yi a Tunusiya

0 321

Mai magana da yawun  ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniyar Ravina Shamdasani ce ta bayyana hakan ga manema labarai a birnin Geniva na kasar Switzerland, inda ta ce matakin na nuni da fin karfi da cin zarafin dan Adam.

Rahotanni sun nunar da cewa a makon da ya gabata ne aka kai samame kan kungiyar lauyoyi ta Tunusiyan, wanda Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana da ya saba ka’idojin dokokin kasa da kasa kan bayar da kariya da kuma ‘yancin lauyoyi.

Wadanda mahukuntan na Tunusiya suka cafke tare da tsareawa dai, sun hadar da ‘yan jarida da kuma masu sharhi kan al’amuran siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: