Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla fararen hula 136 ne aka kashe tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine

0 130

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla fararen hula 136 ne aka kashe tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yara 13 ne ake kyautata zaton na cikin wadanda suka mutu.

Sai dai mai magana da yawun hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sosai.

Kakakin ya ce akasarin wadanda suka mutun sun mutu ne sakamakon manyan hare-hare da aka kai ta sama da tashin bama-bama.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma ce mutane kusan 400 ne suka jikkata a fadan ya zuwa yanzu.

Sai dai alkaluman da gwamnatin Ukraine ta fitar ya yi nuni da cewa fararen hula 352 ne suka mutu sannan dubu 1 da 684 suka jikkata.

A wani lamari mai alaka da wannan, yayin da ake ci gaba da gwabza fada a kasar ta Ukraine, farashin danyen main a cigaba da tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya.

Ya zuwa yanzu danyen man ya kai dala 113 a kowacce ganga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: