Majalisar dattawan Najeriya ta ba da umurnin binciken zarge zargen da shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi na cewa gwamnatin Najeriya na haɗa kai da Faransa wajen kawo cikas ga tsaron ƙasarsa.
Umurnin na zuwa ne bayan wani ƙuduri da shugaban kwamitin tsaro na majaliar, Sanata Shehu Buba ya gabatar, inda ya jaddada cewa babban abin damuwa shi ne yadda Tchiani ya zargi mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa, Ahmed Rufai, da hannu dumu-dumu wajen yi wa ƙasarsa bita-da-ƙulli.
Cikin zarge-zagen nasa, Tchiani ya ce gwamnatin Najeriya na taimaka wa ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa da ke arewa maso yammacin ƙasar, wajen kafa sansanoni a Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi, sannan suna amfani da wasu sansanonin sojoji a Najeriya domin kai hari kan bututun man Nijar da kuma kawo barazanar tsaro a ƙasarsa.
A martaninsa a zaman majalisar, mataimakin shugaban majalisar, sanata Barau Jibrin wanda ya jagoranci zaman ya amince da matsayar da ta buƙaci kwamiti kan tsaron ƙasar da kwaminitin harkokin ƙasashen waje su gudanar da bincike su kuma gabatar da rahoton nan da makonni huɗu.