Majalisar dattawa za ta fara zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan batun sake duba albashin alkalai

0 242

Majalisar dattawa za ta fara zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan batun sake duba albashin alkalai da  alawus-alawus a fadin kasar nan.

Wasikar mai kwanan wata 14 ga Mayu, 2024, ta sanar da AGF cewa ta shirya don gabatarwa Majalisar Dattawa da sauran jama’a bukatar.

Wasikar, wacce ke dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Shari’a, ‘Yancin Dan Adam da Harkokin Shari’a, Sanata Mohammed Monguno, ta ce: “Majalisar Dattawa, a zamanta tayi la’akari da ma’aikatan shari’a (albashi da alawus da sauransu) a bajed 2024. 

A cewar sanarwar, za’a ci gaba da sauraren karar a yau (Litinin) da karfe 12 na dare.

Majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar da shugaban kasa Bola Tinubu ya aike mata, domin duba karin albashi da alawus alawus da sauransu, a karo na uku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: