Majalisar dattawa ta yi kira da a kara yawan kudaden da ake baiwa ‘yan majalisa

0 291

Majalisar dattawa ta yi kira da a kara yawan kudaden da ake baiwa ‘yan majalisar a matsayin kudaden ayyukan mazabu.

Haka nan Majalisar Dattawa ta yi kira da samar da wani kudiri na neman samar da dokar samarwa Mazaba sauran ayyuka na musamman a cikin kasafin kudin shekara-shekara na Tarayya da kuma sauran batutuwa masu alaka da mazabu.

Kudirin dokar da Sanata Babaginda Hussaini na jam’iyyar APC, daga jihar Jigawa ya gabatar a jiya ya gaza tsallake karatu na biyu.

‘Yan majalisar dai sun yi musayar yawu cewa karin kudaden ne za su ba su damar gudanar da ayyukan mazabu a mazabunsu daban-daban da kuma samun kudaden da aka ware a kasafin kudin shekara. A muhawarar da ya gabatar, Babangida Hussaini ya bayyana cewa, aikin mazabar bai ta’allaka ga Nijeriya kadai ba, inda ya kara da cewa hakan na daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa wajen tabbatar da rarraba ci gaban kasa a fadin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: