Majalisar dattawa ta nemi gwamnan CBN Olayemi Cardoso da ya gurfana a gabanta

0 308

Majalisar dattawa ta hannun kwamitinta mai kula da harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso, da ya gurfana a gabanta a ranar Talata.

Gwamnan bankin zai bayyana a gaban majalisar ne domin bayyana halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki da kuma karyewar naira da ake ci gaba da samu a kasuwar hada-hadar kudade.

Shugaban Kwamitin, Adetokunbo Abiru ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jiya Laraba a Abuja, bayan wani zaman sirri da suka yi. Adetokunbo ya ce halin da tattalin arzikin kasa ke ciki, musamman ma hauhawar farashin kayayyaki inda yace yan majalisar sun damu matuka akan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: