Majalisar Dattawa ta gayyaci shugabannin tsaro kan zargin Amurka na ba wa Boko Haram kuɗi

0 126

Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci shugabannin hukumomin bayanan sirri da na tsaron ƙasar da su gudanar da bincike kan zargin da ɗanmajalisar wakilan Amurka Perry Scott ya yi cewa hukumar raya ƙasashe masu tasowa ta Amurka, USAID, na samar da kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.

Majalisar ta zartar da hakan ne bayan da Sanata Mohammed Ali Ndume, ya gabatar da buƙatar binciken.

Ndume ya buƙaci majalisar ta ɗauki maganar da muhimmanci bisa la’akari da iallar da ‘yan ta’adda musamman ma Boko Haram suka yi.

Sanatan ya jaddada cewa cikakken bincike a kan lamarin zai iya kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa a kan yadda ‘yan ta’adda suka iya kaiwa tsawon waɗannan shekaru suna ta’asa a ƙasar.

Leave a Reply