Majalisar dattawa ta gayyaci ministan ma’adanai, Dele Alake, da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar mai kula da ma’adanai ranar Laraba ta mako mai zuwa.
Ana sa ran ministan zai yiwa majalisar bayani kan shirin gwamnatin tarayya na bunkasa fannin da kuma dakile ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin wanda Sanata Sampson Ekong ya jagoranta, ya zargi Dele Alake bisa yin watsi da duk wata gayyata da aka aika masa tun lokacin da shugaban kasa ya nada shi a matsayin ministan ma’aikatar.
Ekong, yayin taron kwamitin a jiya alhamis, wanda ya bayyana damuwarsa kan yadda ministan ya yi watsi da ayyukansa wanda hakan zai kara martabar fannin ma’adinai a kasar nan a idon duniya.
Ya ce rashin mayar da hankali da ministan ya yi a fannin ya kara haifar da cikas ga fannin ma’adanai a kasar nan da Don haka kwamitin ya yi barazanar kin baiwa ma’aikatar kason kudi a shekarar 2024, idan har ministan ya gaza amsa gayyatar da aka yi masa.