A yau Majaslisar Dattawa za ta fara aikin tantance mutanen da Shugaba Buhari ya aiko domin tanancesu da zummar basu mukaman ministoci.
Majalisar ta dattawa zata zauna anar Juma’a da Litinin saboda aikin tantancewar, bayan kuma ta dage tafiya hutunta na shekara da sati 1, wanda a baya aka shirya tafiya ranar Alhamis, domin aikin tantance mutanen 43 da za a nada ministoci.
Shugaban Majalisar ta Dattawa, Ahmad Lawan, shine ya karanta wasikar Shugaba Buhari, bayan zaman majalisar na tsawon mintuna 20 da aka yi jiya kofa a kulle.
Gabatar da sunayen da Shugaba Buhari yayi yana daga cikin kundin tsarin mulki na shekarar 1999, sashe na 147, da 2 cikin baka, kamar yadda aka rubuta a cikin wasikar.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa sunayen da aka gabatar wannan karon sunfi na shekarar 2015 yawa, wadanda aka nada ministoci 36.
Hakan ya biyo bayan alkawarin da Shugaba Buhari yayi na kara yawan ministocin.
Jihohin Anambra da Bauchi da Edo da Kaduna da Kano da Kwara da kuma jihar Legas sun samu mutane 2 kowacce, kuma da ga cikin shiyyoyi 6 dake kasar, Arewa Maso Yamma ce kadai ta samu karin mutane 2.
Shugaba Buhari ya kara yawan mata daga 6 a shekarar 2015, zuwa 7 a wannan karon, kamar yadda mukaman ministocin suka karu zuwa 43. A wannan karon an mika sunayen a watanni 4, kasa da lokacin da aka mika a shekarar 2015.