Majalisar dattawa ta amince da hukuncin kisa ga dillalai da masu shigo da hodar iblis da tabar wiwi

0 230

A jiya Alhamis ne majalisar dattawa ta amince da hukuncin kisa ga dillalai da masu shigo da hodar iblis da tabar wiwi da sauran muggan kwayoyi cikin kasar nan.

Hukuncin kisan ya kuma shafi masana’antun da ke sarrafa kayan mayen, da masu fataucin su, ta kowace hanya.

Majalisar dattijai ta yanke kudurin a zauren majalisar ne bayan tattaunawa kan gyaran fuska ga kudurin dokar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, 2024.

Hukunci a cikin dokar ta baya wadda aka yiwa gyaran fuska a yanzu shine daurin rai da rai.

Hukuncin shigo da muggan kwayoyi ko dillancin su na a sashe na 11 na dokar da ta gabata, wanda Ndume ya nemi a karawa hukuncin tsanani izuwa  hukuncin kisa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: