Majalisar Dattawa ta ɗage zaman tantance sababbin ministocin Tinubu

0 130

Majalisar Dattawan Najeriya ta ɗage zaman da ta shirya yi a yau Talata na tantance sababbin ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaɓa, zuwa gobe Laraba 30 ga watan Oktoba, 2024, da ƙarfe 12 na rana.

Tashar talabishin ta Channels ta ruwaito cewa, majalisar ta matsar da zaman zuwa gobe ne domin bayar da dama ga waɗanda za ta tantance ɗin su kammala dukkanin ayyukan shigar da takardunsu wajen rijista da kuma shirya wa aikin tantancewar.

Mutane bakwai ne shugaban ƙasar ya zaɓa domin naɗa su a matsayin sababbin ministocin, waɗanda ya aika da sunayensu bayan da hukumar ‘yansandan farin-kaya ta DSS ta wanke su bayan gudanar da bincike a kansu.

Mutanen bakwai su ne: Bianca Odimegwu Ojukwu – wadda tsohuwar matar jagoran Biyafara Chukwuemeka Ojukwu ce – ƙaramar ministar harkokin waje, Jumoke Oduwole ministar kasuwanci da zuba jari.

Sauran su ne: Nentawe Yilwatda ministan ayyukan jinƙai da rage talauci, Muhammadu Maigari Dingyaɗi ministan ƙwadago, Idi Mukhtar Maiha ministan kula da dabbobi, Yusuf Abdullahi Ata ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Suwaiba Said Ahmad ministar Ilimi.

Shugaba Tinubu ya zaɓi sababbin ministocin bakwai ne bayan sallamar wasu guda shida, a wani garambawul da ya yi wa majalisar zartarwarsa a makon da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: