Majalisar ƙaramar hukumar Ƴankwashi dake jihar Jigawa ta siyo sabbin na’urorin gwajin cutar Sikila guda 5

0 295

Majalisar Karamar Hukumar Yan Kwashi dake nan Jihar Jigawa ta siyo sabbin Na’urorin gwajin cutar Sikila guda 5 domin tantance Ma’auratan da zasu yi aure domin tabbatar da Lafiyar su da ta Jaririn da zasu Haifa.

Shugaban Karamar Hukumar Hon Mubarak Ahmed, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema Labarai Jawabi a ofishinsa domin bikin cikarsa Kwana 100 akan mulki.

A cewarsa, Majalisar karamar hukumar ta raba Na’urorin zuwa Asibitocin da suke garuruwan Gurjiya da Karkarna da Ringim da Achilafiya da kuma Firji.

Haka kuma Shugaban Karamar Hukumar ya ce a kokarinsa na inganta lafiyar Al’umma, gwamnatinsa ta yiwa mutane 300 Magani kyauta a Asibitoci na yankin.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kakaba Dokar yin gwajin cutar Sikila da HIV dole ga Ma’auratan da zasu yi aure domin dakile yaduwar cutar a sassan Jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: