A jiya ne majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakan shawo kan tsadar rayuwa tare wadda tay mummunar illa ga ‘yan Najeriya.
‘Yan majalisar sun yi wannan kiran ne a lokacin da suka karbi bakuncin ministocin da suka hada da na kudi da kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun da na Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Atiku Bagudu da Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Olayemi Cardoso da shugaban hukumar tara haraji ta tarayya FIRS, Zacch Adedeji, a gaban majalisar.
Zaman ya kasance wani bangare na biyu na muhawara da Tattaunawa wanda majalisar ta gabatar da shi domin tattaunawa da shugabannin ma’aikatu da hukumomin kan manufofin gwamnati.
‘Yan majalisar sun bukaci a yi bayani kan matakan da CBN, da hukumar tattara haraji ta kasa da ma’aikatu ke dauka dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Tun da farko dai sun amince ne da kudirin da dan majalisa Ayokunle Isiaka na jam’iyyar APC, daga jihar Ogun ya gabatar a kan al’amuran da suka shafi jama’a, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakin magance matsalar tsadar rayuwa. Da yake jawabi, dan majalisar wakilai Ahmed Jaha Babawo na jam’iyyar APC, daga Borno yace babu wanda yake bukatar wani dogon bayani domin kowa yasan cewa yan Najeriya na cikin yunwa da talauci.