A jiya ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da wasu kwangiloli guda biyu na gina cibiyar inganta muhalli a karamar hukumar Kana ta Jihar Ribas da kuma asibitin kwararru mai gadaje 100 a Ogoni.
Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi, ya ce, ayyukan sun kasance don sauƙaƙe hanyoyin don magance gurɓata yanayi da dawo da muhalli tare da tallafawa jin daɗin jama’ar da cutar ta shafa a waɗannan yankuna. .
Ya ce an bayar da kwangilar gina cibiyar kwararrun ma’aikata ta CCECC Nigeria Limited, a kan kudi N41,472, wanda za’a kammalawa cikin watanni 24.
Ya ce kwangilar gina asibitin kwararru na Ogoni mai gadaje 100, an bayar da shi ne a matsayin kamfanin Messrs Tannit Medical Engineering Limited, a kan kudi N18,308, wanda shimazai kammalu cikin watanni 24.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce ma’aikatar sufurin jiragen sama ta samu amincewar gina dakin kwanan dalibai mata masu dakuna 150 a kan kudi N2,244, za’a kammala cikin watanni 12.
Ya ce gidan kwanan dalibai da za a gina a Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya, Zariya. Lai Mohammed ya ce majalisar ta kuma amince da Naira 383,968 don siyan motocin aiki guda 13 ga gidan rediyon tarayyar na kasa wanda za’a kammala cikin makonni uku.