Maiduguri babban birnin jihar Borno na daga cikin wurare mafiya tsaro a Najeriya

0 174

Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce Maiduguri babban birnin jihar Borno na daga cikin wurare mafiya tsaro a Najeriya a halin yanzu duk da rikicin Boko Haram da birnin ya yi fama da shi a baya.

Janar Musa ya bayyana haka ne a yau Laraba lokacin da yake ganawa da shugabannin kafofin yada labarai a Abuja.

Ya ce Mutane ne kawai suke ganin kamar babu tsaro a Maiduguri, amma birnin na daga cikin waurare mafiya tsaro a kasar nan yanzu haka. Babban hafsan tsaron na Najeriya ya ce rundunar sojin kasar ta yi bakin ƙoƙarinta cikin shekara daya da ta gabata wajen ganin an ƙara dakushe ayyukan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap

Leave a Reply

%d bloggers like this: