Mai Mala Buni ya amince da biyan Naira miliyan 695.9 a matsayin alawus na Eid-el-Kabir ga ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a jihar

0 184

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da biyan Naira miliyan 695.9 a matsayin alawus na Eid-el-Kabir ga ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a jihar.

Babban sakatare na ofishin shugaban ma’aikatan jihar Bukar Kilo ne ya bayyana haka a Damaturu ranar Talata.

Kilo ya ce za a biya Naira miliyan 375.9 ga ma’aikatan kananan hukumomi da ‘yan fansho, yayin da Naira miliyan 320 na ma’aikatan gwamnatin jihar da ‘yan fansho.

Ya kara da cewa kowane ma’aikaci da dan fansho za su karbi Naira 10,000 da kuma N5,000 bi da bi.

Sakataren din din din ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su maida hankali wajen sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyuka da kuma addu’ar samun nasara ga gwamnatin Buni a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: