Mai Ka Sani Kan Masarautar Ringim?

0 634

Sarkin RINGIM Alhaji Sayyadi Abubakar Mahmud OON, Sarkin farko na Masarautar Ringim a Jihar Jigawa.

An kirkiro masarautar a shekarar 1991 bayan kirkirar sabuwar Jihar Jigawa daga Jihar Kano.

Sarkin Ringim Sayyadi Abubakar Mahmud Ɗa ne ga Tafidan Kano Mahmuda (a lokacin suna karkashin masarautar Kano) kuma jikan Sarkin Kano Usman II. Kakan sa , Sarkin Kano Usman shi ne ya fara hakimcin Ringim a 1904 kafin daga baya ya zama Sarkin Kano a 1919.

Allah ya daga darajar sarautar akan Sarkin yanzu a 1991. Allah ya kara ma Sarki lafiya da nisan kwana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: