Mutanen gari sun hallaka mutum daya da ake zargi da garkuwa da mutane suka kuma lahanta dayan a Jihar Sakkwato.
Dandazon mutanen sun kuma kona Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Kware ta Jihar inda aka tsare mutanen da ake zargi da satar mutane.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce gungun mutane sun yi wa ofishin ’yan sandan tsinke ne suna neman a damka musu wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sanusi, ya ce ana tsaka da bincikar wadanda ake zargi ne mutane suka fara boren a ofishin ’yan sandan cewa dole a mika musu wadanda ake zargin.
Da haka ne zugar mutanen suka fi karfin jami’an da ke ofishin ’yan sandan, suka kona ofishin da motocin ’yan sanda da ke ajiye a wurin.
Ya tabbatar da cewa mutanen suna sun kashe daya daga cikin wadanda ake zargin, dayan kuma suka ji masa rauni.
Sai dai ya ce ba a kama kowa ba, amma ana kan gudanar bincike a kan lamarin.