Maganar Shugaba Buhari Bayan Nijeriya Tayi Bankwana Da Polio

0 212

Shugaba muhammadu Buhari ya taya yan najeriya murna biyo bayan bankwana da kasar tayi daga cutar shan inna, yayin nuna godiyarsa ga wanda suka taimaka na gida dana waje, bisa jajircewarsu na ganin sun raba kasar da cutar yaran.

A jawabinsa shugaban kasa ta bakin mataimaki na musamman wajen yada labarai da hulda da jamaa, Garba shehu, yace wannnan nasara zata sanyaya ruhin yan kasar.

Haka kuma Ya yabawa maza da mata da suka bada gudummawa a fannin lafiya, wanda ya alakanta nasarar da jajircewarsu da goyon bayansu wajen kawo karshen jinyar.

Buhari yace wannan nasara ba ita kadai alummar kasar suka cimmaba a lokacin mulkinsa, kuma wannan abune da baza a taba mantawa dashiba a idan aka tina mulkinsa, wannan nasara ta kawo daidaito wajen ciyar da kasar gaba a fannin lafiya tun a shekarar 2015.

Leave a Reply

%d bloggers like this: