Ma’aikatan lantarki na Kaduna sun dakatar da yajin aiki

0 104

Hadakar ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta jihar Kaduna sun jingine yajin aikin da suka ɗauki kwanaki suna gudanarwa a jihar.

Yajin aikin ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a jihohin Kaduna da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi.

Matakin na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Sanata Uba Sani ya sanya baki tare da zama da duka ɓangarorin biyu.

Yayin jagorantar zaman Gwamna Uba Sani ya nuna matuƙar damuwa halin da al’umma da masu sana’o’i suka shiga sakamakon yajin aikin.

Sannan ya yi kira ga duka bangarorin biyu su sake nazarin matakan da suka ɗauka.

Daga ƙarshen ganawar ma’aikatan sun amince su maido da wutar lantarki da suka katse tsawn kwanaki a Kaduna da sauran jihohin da ke samun wutar daga kamfanin.

Haka kuma ɓangarorin biyu, sun cimma matsayar zama tare domin tattauna yadda za a rage ma’aikatan kamfanin.

Ƙungiyar ma’aikatan dai ta shiga yajin aikin ne bayan da ta zargi kamfanin rarraba lantarki na Kaduna Electric da korar wasu ma’aikata kusan 900 da ta ce an yi ba bisa ƙa’ida ba.

Kamfanin dai ya ce ma’aikatan da ya kora 450 ne ba kamar yadda ƙungiyar ke iƙirari ba, kuma ya kare matakin da cewa ya yi hakan ne sakamakon rashin kuɗin da yake fama da shi.

Yajin aikin dai ya janyo wa masu sana’o’i da dama mummunar asara a harkokinsu.

Leave a Reply