Ma’aikatan hakar ma’adinai 31 ne suka mutu sakamakon rugujewar wani wajen hakar zinare a Sudan

Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 31 ne suka mutu, takwas kuma sun bace a yau a kasar Sudan, sakamakon rugujewar wani wajen hakar zinare.
Shugaban Kamfanin Albarkatun Ma’adanai na gwamnatin kasar a yammacin Kordofan, Khaled Dahwa, ya ce iftila’in ya afku ne a kusa da Nuhud, wani gari mai tazarar kilomita 500 daga yammacin birnin Khartoum.
Wani jami’in kamfanin ya ce masu hakar ma’adinai hudu sun mutu a wannan mahakar ma’adanan a watan Janairu.
A dai nahiyar Afirka, kwamitin sasanto da aka kafa domin binciken laifuffuka da cin zarafi da tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya aikata, ya bayar da shawarar a gurfanar da tsohon shugaban.
Kwamitin wanda aka kafa karkashin wata doka a shekarar 2017, ya na bincike tare da tattara bayanan take hakkin dan adam a karkashin mulkin Yahya Jammeh na shekaru 22.
Yahya Jammeh, tare da wasu mutane dayawa da ake zarginsu, an same su da laifi a mafi yawan zarge-zargen kuma an bayar da shawarar a gurfanar da shi gaban kuliya.