Liverpool ta shigar da ƙarar wasan da ta yi da Everton

0 386

Mahukunta a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool sun shigar da ƙara neman bayanin yadda aka yi alƙalancin wasan da suka buga da Everton jiya.

A cewar zakarun na Nahiyar Turai suna ganin kamar akwai matsala a yadda akayi amfani da na’urar dake taimakawa alkalin wasa VAR saboda haddasa ruɗani wajen yanke wasu hukunce-hukunce a wasan hamayyar.

Don haka ne Liverpool suke buƙatar a amsa musu wasu tambayoyi guda 3;

1. Menene dalilin da yasa ba’a duba yadda mai tsaron ragar Everton yayi mummunan taku ga ɗan wasanta Virgil van Dijk a na’ura ba?

2. Shin wane ɓarin jikin ne na Mane yake a cikin ma’aunin satar gida (offside)?

3. A daidai wane lokaci ne ake amfani da layin auna satar gida (offside)? har a gane wani ya shiga ko bai shiga ba?

A bayyana ne yake a fuskar yan wasan Liverpool da magoya baya cewa basu ji dadin yadda wasan ya kare a 2 -2 ba musamman ma da yake Henderson ya jefa kwallon da aka kashe a gab da tashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: