Labarin gawurtacciyar matar da ke noma gona mai fadin filin kwallo 1000

0 303

Nike Tinubu mace ce mai shekaru 59 a duniya. Ba a Jihar Oyo kadai inda ta ke ba, Nike ko a Najeriya a yanzu haka ta na a sahun farko na kasaitattun manoma rogo da kuma sassafa garin alabo.

Ita ce Shugabar Kamfanin Sarrafa Garin Rogo na Egaleson Farm. Fadin gonar da ta ke noma rogo gantamau ya kai hekta 1800.

Kun fa ji mace mai himma, ba Tsumburau mai noma kuyye goma na masara ba.

Nike gawurtacciya ce, saboda a gonar ta da masana’antar da ta ke sarrafa gari, ta na da ma’aikata har 53 da ta ke biyan su albashi duk wata. Sannan kuma akwai majiya karfi tsakanin 11 zuwa 19, masu zuwa su yi aiki a biya su ba na dindindin ba.

Kun fa ji manyan mata masu himmar noma. Albashin ma’aikatan ta ma kadai ya fi karfin jarin wani gidan biredin zamani.

Da Nike mace ce, to sai dai mu kira ta ‘Sarkin Noma Jimrau, ko Kosau, ko kuma Nomau. To ita ce fa ta fara kafa Kungiyar Masu Masana’antun Sarrafa Rigo.

Da a zamanin baya aka yi Nike a nan Arewa, to za ta yi gogayya da irin su Sarkin Noma Ali Na Mani Kotoko, ko irin Garba Bajinin Maidamma, Ko Sarkin Noma Turbe (mazan yau da gobe). Kai, ina ganin sai dai a hada Nike da Sarkin Noma Alasan Mai Walkin Maraki.

Da kadan-kadan ta fara sana’anar sarrafa garin rogo, har ta yi karfin rika bai wa masu noman rogo kudi su rika kawo mata rogo gantamau ta na sarrafa shi zuwa garin alabo.

“Amma sai rogo ya rika yi mana karanci, saboda idan na bai wa manoma kudi su kawo min rogo, sai su karbi kudin kuma su karkatar da rogon zuwa wani wuri, sannan kuma sai sun juya kudi na kafin su biya ni.

“Daga nan na yi kumumuwa ni ma na shiga harkar noman gadan-gadan.”

Kun fa ji mace mai zuciya da himma, sai ka ce Sarkin Noma Mamman Maci Sabra.

Da ya ke tun cikin shekarar 2005, zuwa 2013 har Nike ta yi gawurtar da ta kafa ma’aikatar sarrafa rogo tare da hadin guiwa da Gwamnarin Jihar Lagos.

Babban aikin wannan masana’anta a Epe mai suna Eko Cassava Factory, shi ne koya wa matasa harkar sarrafa rogo da kuma karfafa su.

Kun fa ji mace mai zuciyar noma. Irin haka fa a can shekarun baya a Kasar Hausa, Gojen Noma ke tara karti matasa majiya karfi kamar 40. A duka noma a mirgina kuyye a nausa yamma, ba a tashi sai rana ta fadi.

“Na kuma maida hankali sosai wajen karfafa mata a wannan sana’a. Kuma na kashe wa matasa da yawa guiwar yin hijira zuwa biraje su ka ragaitar banza. Saboda na rika koya masu sana’ar da a cikin karkarar su ma za su iya samun kudin da idan sun je birni ba samun kamar su za su yi ba.” Inji Nike, uwar manoma.

Matasan da Nike ta koya wa sana’ar sarrafa rogo zuwa garin fulawa ko garin alabo sun kai 700, kamar yadda ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Wannan fa fannin sarrafa rogo kadai kenan. Ba mu kai fannin noma ba tukunna.

Sai dai ta yi korafin cewa gwamnati ba ta maida hankali wajen bunkasa harkokin noma ga mata.

Ta ce Bankin Manoma (BOA) kawai suna ne a baki, idan ma har yanzu ya na aiki, to bai san aikin shi ba. “Saboda BOA bai san komai ba a fannin kasuwancin noman da ake yi a samu makudan kudade.” Inji Nike.

Nike ta yi wa wakilin mu karin hasken yadda ake adana sinadaran kayan rogo har ya shekara bai lalace ba.

Sannan kuma ta bayar da shawarwarin yadda za a fita daga tsallen-badaken da manoma ke yi a duk shekara wajen gaganiyar samun wadataccen takin zamani. Duk da ya ke dai ita ta ce ba ta amfani da takin zamani kwata-kwata.

Batun tsaro kuwa ta ce sau da yawa idan ma’aikatan ta su ka ji labarin an kai hari wasu wurare, sai su ki fitowa.

“To kuma ka san idan masu yi maka noma ba su fito ba, har aka yi kwanaki, abin da ka shuka ba zai yi kwari sosai ba.

“Sannan mai manyan gonaki kama ta idan ya ce zai dauki jami’an tsaro masu kula da tangamemiyar gona, ko ya gine ta da katanga da waya, to abin da ake nomawa zai kara tsada kenan.”

‘Yadda Na Ke Noma Gona Mai Fadin Filin Kwallo 1000’ – Nike, uwar manoman rogo

“Ni ba ni da matsakar gonakin noma. Gonaki na sun kai fadin hekta 1800, kwatankawacin filin kwallo guda 1000.

Wani abin burgewa da Nike, ‘yar caraf ce, kamar ka hure ta ta fadi kasa. Amma duk da haka ta zama ‘raina kama ka ga gayya a cikin maza, ba ma a matan kadai ba.

“Ina fuskantar nuna min bambancin jinsi sosai. Ko baya-bayan nan ma an je wani taro da gwamna, amma saboda matsala cutar korona, aka ce ba a so a cunkushe da yawa. Sai ana ce wasu su fita.

“Mata ba su da yawa a wurin, duk sai su ka fice, sai ni kadai. Wani hadimin gwamna ya zo ya ce min, “to ke za ki jawabi ne da ki ka zauna? Ai gara ki fita kawai. Ni dai ko kallon sa ban yi ba.

“Can fa Gwamna ya na jawabi aka ji ya ambaci suna na har sau biyu ya na jinjina min. Nan kuma bayan an tashi taro sai kowa ya rika neman ya zama aboki na.

“Ka san dalilin kallon rainin da aka yi min da farko? Kawai don an gan ni ‘yar firit, kamar ruwan aski.” Inji Nike uwar manoman rogo.

Asalin labarin;

Leave a Reply

%d bloggers like this: