A karon farko tun watan Afrilu, yawan wadanda suka kamu da corona a Najeriya cikin rana guda yayi kasa da 100.
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar da samun sabbin mutane 79 a jiyar Lahadi da dare, adadi mafi karanci a cikin kusan watanni biyar.
An samu sabbin mutanen a jihoshi 12 da babban birnin tarayya.
- Mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin sama ya yi hatsari a Kazakhstan
- Gwamnan Kebbi ya bada motocin shinkafa guda 3 don bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
- Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a jihar
- Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da suka fi dogaro da lamuni daga IMF a Afirka
- Gwamnatin Tarayya ta wanke mutane 888 daga zargin ta’addanci
An kuma samu rahoton sabbin mutane 4 da cutar ta hallaka a jiyan, inda jumillar wadanda cutar ta kashe ya kai dubu 1 da 82.
Kazalika, da mutane 64 da suka warke kuma aka sallamesu a jiya, an samu rahoton karancin wadanda suka warke daga cutar a rana guda tun ranar 21 ga watan Mayu.
Daga cikin mutane dubu 56 da 256 da yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar corona a jihoshi 36 da babban birnin tarayya, mutane dubu 44 da 152 sun warke.