Kyakkyawan Labari: Gwamnatin Nijeriya zata ƙirƙiro ayyuka miliyan 10

0 354

Gwamnatin Tarayya za ta kirkiri ayyuka kimanin miliyan 10 a bangaren aikin gona, karkashin shirin samar da abinci da ayyukan yi.

Ministan aikin gona da raya karkara, Sabo Muhammad Nanono, ya sanar da haka a Abuja a wajen taron manema labarai na ministoci, gabannin bikin ranar abinci ta duniya.

Ana gudanar da bikin ranar abinci ta duniya a ranar 16 ga watan Oktoban kowace shekara a kasashe sama da 150 a fadin duniya domin wayar da kai da fadakar da mutane dangane da batun fatara da yunwa.

Minstan yace shirin samar da abinci da ayyukan yi, wani tsagi ne na shirin dorewar tattalin arzikin Najeriya na shugaban kasa Muhammadu Buhari, an kaddamar da shi a watan Yuli domin kara yawan filayen da ake nomawa a kowace jiha tare da bayar da bashin da babu kudin ruwa ga manoma, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: