Kwastam sun kama manyan kwantenoni guda 9 makare da makamai da alburusai da muggan kwayoyi

0 175

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato kwastam ta sanar da kama manyan kwantenoni guda 9 makare da makamai da alburusai da muggan kwayoyi da kuma kayan gwanjo da aka ɗauko su daga kasar Turkiyya.
Shugaban hukumar Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin bayani a gaɓar ruwan Onni da ke Fatakwal na jihar Rivers.
Mista Adewale ya ce darajar kayayyakin da aka kama ta kai naira biliyan 13 da miliyan 900.
Shugaban ya kuma ƙara da cewa abin mamakin shine yadda masu laifin suka yi nasarar fitowa da kayan daga kasar Turkiyya suka kuma iso da su Najeriya ba tare da an iya kamasu ba, la’akari da yawan kayan.
Yayin da yake bayani, ya yabawa jami’an hukumar da kuma wasu jami’an sirri da ke aiki a gaɓar ruwan, yana mai cewa da wannan bayani ne aka yi amfani wajen kama kayan. Da fari dai wanda ke da alhakin shigo da kayan ya so bi ta barauniyar hanya don ficewa da su daga tashar, amma kuma da haɗin kan jami’an hukumar aka kama shi.
Bayanai sun nuna cewa darajar kudin fiton kayan kadai ya zarta Naira biliyan 4 da miliyan 200, kuma tuni aka kama mutane uku da ke da hannu a safarar kayayyakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: