Kwankwaso yayi Allah wadai da rashin wutar lantarki a Arewa

0 141

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jin daɗinsa kan rashin wutar lantar a mafi yawan jihohin Arewa.

Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce, “Abin takaici ne a ce mafi yawan yankunan Arewa suna zaune cikin duhun rashin wutar lantarki saboda tangarɗa a layin lantarkin 330kV wanda ya ɗauko wuta daga Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ne yake ba jihohin Kano da Kaduna, da layin da yake ba Bauchi da Gombe da wasu jihohin arewa maso gabas wuta.

“Matsalar ta ƙara ta’azzara ne saboda yanayin tsadar man fetur da ake ciki a Najeriya, wanda ya tilasta wa kamfanoni da kasuwanci da dama suka durƙushe.

Sannan lokacin da aka ɗauka ba a magance matsalar ba, ya nuna cewa akwai matsala a ɓangaren makamashin Najeriya,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa akwai buƙatar a ɗauki mataki domin guje wa sake aukuwar lamarin, ta hanyar nemo wasu hanyoyin makamashin.

“Ina ba jihohin da ƴan kasuwa shawarar su zuba kuɗi a wasu hanyoyin samar da makamashin domin rage ta’allaƙa da hanyar makamashi guda ɗaya,” in ji Kwankwaso.

Leave a Reply

%d bloggers like this: