Kwankwaso ya caccaki Tinubu kan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

0 56

Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Shugaban Ƙasa Bola Tinubu game da dokar ta-ɓaci da ya saka a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.

CIkin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis da dare, Kwankwaso ya siffanta matakin na Tinubu “mai haɗari ga dimokuɗiyya”.

A ranar Juma’a ne Tinubu ya sanya dokar da ta dakatar da Gwamna Fubara, da majalisar dokokin jihar tare da maye gurbin gwamnan da kantoman riƙo saboda abin da ya kira “rashin doka da oda” sakamakon rikicin siyasa tsakanin Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.

“Ina ganin rikicin siyasar da ake ciki a Rivers bai isa ya sa a ayyana sashe na 305(1) na kundin tsarin mulki ba,” in ji shi.

“Abin da ya fi damu na ma shi ne yadda majalisun dokokin ƙasa suka amince da buƙatar shugaban ƙasa. Na yi fatan ba za su yarda da wannan abu da ya karya doka ba…Wannan mataki nasu zai kawo wa dimokuraɗiyyarmu cikas.”

Leave a Reply