Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP ta kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana kwarin gwiwar sa na cewa kotun koli zata yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano cikin adalci.
Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a jiya litinin yayin taron addu’ar da magoya bayan jam’iyyar suka gudanar a gidansa dake Miller Road cikin Birnin Kano.
Taron addu’ar wanda gwamnatin jihar ta shirya, nada nufin samun nasara ga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf a kotun koli, yayin da ake dakon sakamakon hukunci kan shari’ar gwamnan jihar.
Kwankwaso, yace alamu sun nuna cewar alkalan kotun koli mutane ne masu daraja don haka za su yanke hukuncin bisa adalci da gaskiya. Kwankwaso ya kara da cewa dole ne a tunatar da masu rike da madafun iko cewa adalci shine hanyar samun ci gaba yayin da rashinsa zai kawo rudani da rikici wanda zai hana ci gaba mai ma’ana.