Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya raba kudi sama da Naira Milyan 12 da dubu 2 a matsayin zakka ga mutane marasa galihu a gundumar Birniwa dake nan jihar Jigawa.
Sakataran Kwamitin, Injiniya Ismail Garba shine ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan raba zakkar.
Ya kuma ce kayan da suka karba daga Manoma da dai-daikun masu kudi da makiyaya ya hada da buhunan gero 594, buhun wake 1,da mudu 17 na hatsi, sai kuma tumakai 9 da awakai,da Saniya 1, da kuma buhun Shinkafa 1 sannan da tsabar kudi Naira dubu 26.
Babban limanin Masarauta Mallam Yusuf Abdulrahama yayi kira ga muslmi da suna fitar da zakka a matsayin ta na daya daga cikin rukunan Musulunci.
Ana sa jawabin Hakimin Birniwa, Sarkin Arewan Hadejia Alh Aliyu Abubakar ya bukaci al’ummar yankin da suna bada zakka tare da yin alkawarin kara kaimi wajen karbar zakkar.
- Comments
- Facebook Comments