Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya raba buhunan shinkafa 1,564, da na gero 800, tare da na dawa 232, wanda darajarsu ta kai sama da naira miliyan dari (N100m) ga mabukata a yankin Jabo na karamar hukumar Kafin Hausa.
Shugaban kwamitin, Talban Hadejia, Barrister Abdulfatah Abdulwahab ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon a kauyen Inkaibo, inda wakilinsa, Wakilin Yankasuwa, Alhaji Muhammed Garba Dankundi, ya yaba da kokarin kwamitin yankin wajen tattara zakka da wayar da kan jama’a kan muhimmancin zakka a wannan lokaci na tsadar kayan abinci.
Sakataran kwamitin, Injiniya Isma’ila Garba Barde, ya shawarci masu cin gajiyar kayan abincin da su yi amfani da su wajen ciyar da iyalansu musamman a lokacin watan Ramadan, tare da yin addu’a ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
Hakimin Jabo, Durbin Hadejia, Alhaji Adamu Daudu Zakar, ya gode wa masarautar Hadejia bisa tallafin da suke ba yankin, yayin da Malaman addini Dr. Umar Nasarawa da Malam Ibrahim Shamakeri suka yi wa’azi kan muhimmancin zakka a Musulunci.