Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya karba tare da raba zakkar Naira Miliyan 132

0 292

Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya karba tare da raba zakkar Naira Miliyan 132 ga mabukata a 2023.

Shugaban kwamitin Barista Abdulfatah Abdulwahab Tahir Talban Hadejia ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon zakkar a fadar sarkin Hadejia.

Yace fiye da masu karamin karfi Dubu Shida ne suka amfana da zakkar da suka hadar da marayu da dattijai da masu bukata ta musamman.

Barista Abdulfatah Tahir ya bayyana muhimmancin da zakka take dashi a addinin musulunci , tare da bukatar masu hali su rinka bada zakka domin tsarkake dukiyoyinsu.

A jawabinsa na kaddamar da rabon zakkar ta bana, mai martaba sarkin Hadejia Alhaji (DR) Adamu Abubakar Maje ya yabawa kwamitin zakka na masarautar bisa kokarinsa na Tarawa da kuma rabon zakka a bara inda ya yi fatan zai kara kokari a bana Mai Martaba Sarki ya kaddamar da rabon zakkar Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Biyu ga masu karamin karfi 120.

Leave a Reply

%d bloggers like this: