Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya samu nasarar kama wani mutum bisa laifin yin algus a manja a garin Jahun

0 111

Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya samu nasarar kama wani mai suna Jamilu Abdullahi a kofar babban asibitin Jahun bisa laifin yin algus a manja.

Shugaban Hukumar, Mallam Farouk Abdallah, ya sanar da hakan a wata sanarwa inda yace an samu mutumin ne da laifin hada koko da manja a garin Jahun.

Yace tuni kotun tafi da gidanka ta kwamitin ta zartar masa da hukuncin daurin watanni 6 a gidan gyaran tarbiyya ko kuma zabin biyan tarar naira dubu 60.

Ya kara da cewa kotun ta bashi wa’adin kwanaki 30 domin daukaka kara.

Farouk Abdallah ya kara da cewar tuni kotun ta kwace manjan tare da gargadin cewar muddin ya sake aikata irin wannan laifi zai tafi gidan maza na watanni 3 kafin fara sabuwar sharia.

Ya kuma ce hukuncin zai kasance izna ga masu yin algus a kayayyakin abinchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: