Kwamitin da aka kafa domin bincikar El-Rufa’i ya miƙa sakamako

0 240

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sakamakon bincikensa a yau.

Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i.

Lokacin da ya gabatar da rahoton a jiya Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa’i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo ba ko kuma ba a bi ƙa’idoji wajen kashe su ba.

Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa’i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi.

Sai dai tsohon gwamnan ya ce binciken da majalisar jihar ta ba da shawarar a yi kan gwamnatinsa “bi-ta-da-ƙulli ne kawai na siyasa”.

Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda suka fi yawan bashi a kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: