Sabon kwamishinan ‘yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ya kai ziyarar gani da ido kasuwar Kwalema dake unguwar Dakata, inda aka samu tashin gobara a safiyar larabar nan.
Gobarar ta kone shaguna da dama a kasuwar, wanda hakan ya janyo asarar dukiya mai tarin yawa.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bada umarnin gudanar da bincike don gano dalilin tashin gobarar.