Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi na Jihar Bauchi ya bada shawarar bada fifiko ga Ilimin Makiyaya dan kawo karshen yan bindiga

0 196

Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi na Jihar Bauchi Dr Aliyu Tilde ya bada shawarar bada fifiko ga Ilimin Makiyaya a matsayin hanyar kawo karshen hare-haren yan bindiga a kasar nan.

Dr Aliyu Tilde wanda a kwanan aka nada shi Kwamishinan Ilimin Jihar ta Bauchi, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Bauchi.

Kwamishinan ya gana da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Ilimin Makiyaya ta Kasa Farfesa Bashir Usman, inda ya bashi tabbacin cewa zai taimakawa shirinsa na bada fifiko ga Ilimin Makiyaya.

Kwamishinan ya ce fiye da shekaru 5 da suka wuce, ayyuka 7 ne kawai hukumar Ilimin Fulani ta Jihar Bauchi tayi nasarar aiwatarwa daga cikin Makarantu 463 da suke Jihar, kuma suma Hukumar ce ta kasa ta aiwatar da guda 3.

Dr Tilde ya ce kimanin Makarantun Makiyaya 463 ne akayi watsi dasu a jihar fiye da shekaru, wanda hakan yana daga cikin dalilan da ya sanya mafiya yawan yan bindiga da masu Garkuwa da mutane yan kasa da shekaru 30 ne.

Kazalika ya ce gwamnatin jihar Bauchi zata cigaba da bada fifiko ga Ilimin Makiyaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: