Kwamandan mayakan rundunar RSF ya miƙa wuya tare da wasu dakarunsa

0 170

Rundunar sojin Sudan ta ce ɗaya daga cikin kwamandan mayakan rundunar RSF Abuagla Keikal, ya miƙa wuya tare da wasu dakarunsa, wanda shi ne na farko da aka samu wani babban jami’inta da yayi, tun bayan da ɓangarorin suka faro rikici da juna a tsakiyar watan Afrelun shekarar da ta gabata.

Rundunar sojojin Sudan wacce a ƴan kwanakin nan ta bayar da rahotan fara samun nasarar kwato wasu yankuna na babban birnin ƙasar Khartoum, ta ce Keikal ya ɗauki matakin ne sakamakon yadda rundunar RSF ta sauka daga kan tsarin da aka samar da ita.

Wasu daga cikin masu goyon bayan sojojin Sudan, sunya saka hotunan Keikal da ke jagorantar rundunar RSF a kudu maso gabashin jihar El Gezira, a kafofin sada zumunta, bayan sanar da matakin da ya ɗauka.

Kawo yanzu dai rundunar RSF da ta kwace iko da sassan ƙasar da dama da kuma shi kansa Keikal, basu ce komai game da lamarin ba. Rikicin na Sudan ya sanya sama da mutane miliyan 10 barin muhallansu tare da jefa wasu da dama cikin matsananciyar yunwa, lamarin da ya sanya Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yakin da ake gwabzawa a Sudan din tsakanin sojoji da dakarun RSF, ya haifar da ɗaya daga cikin matsalolin ayyukan jin kai mafi muni a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: