Kwalliya Na Biyan Kuɗin Sabulu Kan Rufe Iyakokin Najeriya – Buhari

0 381

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da matakin gwamnatinsa na wucin gadi kan rufe kan iyakokin kasar na kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawa da wata tawagar kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, da kuma manoma a Abuja, inda ya ce a halin da ake ciki tattalin arzikin ƙasar nan ya soma amfana da matakin rufe iyakokin, don yakar matsalar shigar da kayayyaki cikin kasar ta hanyar fasakauri.

A baya bayan nan dai kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ECOWAS, ta shawarci gwamnatin tarayya ta janye matakin na rufe kan iyakokinta, saboda illar da matakin zai yiwa shirin yankin na yammacin nahiyar ta Afrika, na gudanar da tsarin hada-hadar kasuwancin bai daya.

Sai dai shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na nan kan bakanta na goyon bayan tsarin kasuwancin bai daya tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS, da kuma nahiyar Afrika baki daya, yarjejeniyar da ya sanyawa hannu a watannin baya.

Sai dai shugaban ya ce tilas a gudanar da tsarin kasuwancin na bai daya, bisa tsarin doka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: