Kwalejin Fasaha ta Binyaminu Usman ta gudanar da bikin rantsar da sabbin dalibai 1,036

0 196

Kwalejin Fasaha ta Binyaminu Usman ta gudanar da bikin rantsar da sabbin dalibai dubu daya d talatin da shida na zangon karatu na 2023/2024.

A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a harabar kwalejin, shugaban kwalejin Dr Bashir Garba Muktar ya ce kwalejin ta samu gagarumin cigaba a bangarori daban-daban bisa tallafawar gwamnatin jiha da kuma asusun tallafawa Ilmi na kasa TETFUND.

Yace asusun tallafawa Ilmi na kasa ya dauki nauyin karatun malaman kwalejin kusan guda hamsin domin yin karatun digirin masta da kuma digirin Digirgir da kuma daukar nauyin malaman zuwa tarukan karawa juna sani a ciki da wajen kasar nan.

Dr Bashir Garba Muktar ya kuma yabawa gwamnatin jiha bisa gagarumin sauye sauye da ta samar a kwalejin.

Ya kuma roki da a samar da Karin ma’aikata da kayayyakin koyo da koyarwa.

A jawabinsa shugaban hukumar gudanarwar kwalejin ta hannun daya daga cikin mambobin hukumar Hajia Mariya Miko ta taya sabbin daliban murnar samun damar yin karatu a kwalejin.

Inda ta yi fatan zasu kiyaye da dokoki da kuma kaidojin karatu na kwalejin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: